Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon

Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila

Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai.

Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa  karshen shekarar 2025.

Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta.

“Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen shekara ba, za mu sake yin aiki da karfi a Lebanon, za mu kwance damarar su.”in ji shi.

Katz ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta lamunci abin da ya kira barazana ga matsugunan da ke kan iyakar Lebanon ba.

“Ba za mu yarda da duk wata barazana ga mazauna arewa ba, kuma za a ci gaba da aiwatar da doka har ma da kara yin amfani da karfi.”

A halin da ake ciki dai Washington na matsawa kasar Lebanon lamba kan ta tilastawa kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai, ko da kuwa hakan yana tattare da hadarin fadawar kasar a cikin yakin basasa, kuma ta fito fili ta goyi bayan barazanar da Isra’ila ke yi, tana mai gargadin cewa Lebanon na fuskantar wani babban hari idan har Hizbullah ba ta mika makamanta ba.

A yayin da yake mayar da martani game da batun da ake yi, dan majalisar dokokin Lebanon Hassan Fadlallah ya jaddada cewa, babu inda za a yi wata tattaunawa ta siyasa da Isra’ila yayin da take ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Fadlallah ya ce, har yanzu ba a gabatar da wata shawara ta siyasa ga kasar Labanon da za ta iya dakatar da kai hare-haren ‘yan mamaya yadda ya kamata ba, yana mai yin Allah wadai da tsoma bakin kasashen yammacin duniya da kuma Amurka suke yi a cikin harkokin cikin gidan kasar ta Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments