Shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas, Isma’ila Haniyyah ya bayyana cewa; Kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa mutanen Gaza da sauran laifukan yakin da suke tafkawa, suna nuni ne da yadda su ka ci kasa, su ka kasa cimma manufofin da su ka shata.
Isma’ila Haniyyah wanda tashar talabijin din “almayadeen” ta yi hira da shi ya kara da cewa, abubuwan da suke faruwa a fagen diplomasiyya da ‘yan sahayoniyar yana nuni ne da yadda suka zama saniyar ware a duniya wanda ba su taba fuskantar irinsa ba a baya.
Dangane da tattaunawar da ake yi akan makomar yaki, Isma’ila Haniyya ya ce, kungiyar ta Hamas tana nan akan sharuddan da ta gindaya tun da fari, da su ka kunshi ficewar sojojin mamaya dgaa Gaza, da komawar Falasdinawan da aka tilasatawa yin hijira zuwa gidajensu.
Wannan hirar da shugaban kungiyar ta Hamas, an yi ta ne dai kwanaki biyu bayan da sojojin HKI su ka kashe ‘ya’yan da jikokin Isma’ila Haniyyah su shida.