Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa; Manyan kasashen duniya masu girman kai suna kiyayya ne da duk wani cigaba da jamhuriyar musulunci ta Iran za ta samu.
Har ila yau Salami ya kuma ce; A halin yanzu muna ganin yadda Haramtacciyar kasar Isra’ila take yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da shekar da jininsu, haka kuma mutanen Lebanon, da hakan ya tabbatar da cewa hakkin bil’adama ba shi da wata kima a idon kasashe masu girman kai.
Muhamamd Islami wanda ya gana da manajojin hukumar Radiyo da Talbijin na kasa ‘yan Basij,ya yi bayani akan cigaban da Iran ta samu a fagen fasahar makamashin Nukiliya, sannan ya kara da cewa wajibi ne kafafen watsa labarun kasar ta Iran su rika bayani akan nau’oin cigaban da aka samu a wannan fage na fasahar makamashin Nukiliya.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta Iran ya kuma ce, Iran tana nan akan alkawulan da ta dauka, amma daya bangaren sun take dukkanin alkawullan da suke kansu.