Islami: Iran Ba Zata Daina Tace Yuranium A Cikin Kasarta Ba

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Ba za su daina sarrafa Sinadarin Yuranium a Iran ba, kuma ba za su miƙa Yuranium

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Ba za su daina sarrafa Sinadarin Yuranium a Iran ba, kuma ba za su miƙa Yuranium din ga wata kasa ba

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) ya jaddada cewa: Sarrafa Siradarin Yuranium muhimmin bangare ne na tsarin Shirin makamashin nukiliya kuma ba za su yi watsi da shi a kowane wane irin hali ba.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, Muhammad Islami, shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran “AEOI”, ya bayyana a yayin wani taron tunawa da mahaifiyar shugaban Hukumar Tsare-tsare da Kasafin Kudi cewa: “Sarrafa Sinadarin Yuranium haɓaka muhimmin bangare ne na tsarin shirin makamashin nukiliya, kuma ba za su yi watsi da shi a kowane hali ba. Ta yaya kasa za ta iya da’awar cewa tana da masana’antar makamashin nukiliya idan ba ta da wurin farawa na tsari? Masana’antar makamashin nukiliya karfi ne na kimiyya da fasaha.”

Ya ci gaba da cewa, “Amurkawa da kansu, ciki har da shugaban kasa na yanzu Trump sun fifita fasahar makamashin nukiliya a cikin takardun ci gaban kasa, tsaron kasa da kuma dukkan kasashe suna bin shirye-shiryen makamashin nukiliyarsu cikin sauri.”

Shugaban AEOI ya fayyace cewa: Wadannan da’awar karya ce da makirci Amurkawa ke yi. Abin da ya tabbata shi ne ci gaban kasa; mutanen Iran ba koma baya suke so ba, sai dai zama mutane masu daraja da hazaka a fagen ci gaban kimiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted