IRGC:Idan Amurka Ta Sake Kai Kawo Hari Za ta Canza Makaman Yakinta

dakarun kare juyin musulunci sun ce zasu canza makaman yakinsu idan Amurka ta sake kawo hari

kakakin dakarun kare juyin musulunci na iran bergediya janar Hussain mohebbi ya bayyana a yau litinin cewa idan kasar Amurka ta sake kawo hari to za ta canza taswira da kuma wasu makaman da za ta yi amfani da su wajen mayar da martani .

yace iran zata fitar da sabbin makamanta da sauran kayayyakin soji masu karfin gaske,da zasu sha mamaki, kuma ya bayyana wasu yankuna da kasar Amurka ta sha kaye a yakin da ta kaddamar kana kasar iran

Amurka da isra’ila sun tafka laifukan yaki kan kasar iran na tsawon kwanaki 12 a watan yuni shekara ta 2025 a karo na biyu kuma ta kaddamar da hare hare a ranar 28 ga watan fabarerun shekara ta 2026 inda ya kwashe kwanaki 40 ana yi da kawo karshe a farkon watan aprilu.

a dukkan yake yaken iran ta tsaya kyam wajen mayar martani da hakan ya tilasta musu amincewa da tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted