IRGC ta yi Allah wadai da tsoma bakin Trump a harkokin cikin gida na Iran

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da tsoma bakin shugaban Amurka Donald Trump a harkokin cikin gida na kasar.

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da tsoma bakin shugaban Amurka Donald Trump a harkokin cikin gida na kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, IRGC ta jaddada cewa, kamar ayyukan tayar da zaune tsaye da makiya Iran suka yi a baya, laifukan tayar da zaune tsaye da ‘yan ta’adda suka aikata a baya-bayan nan, wadanda Amurka da Isra’ila ke goyon baya, za su cutura gaba daya.

IRGC ta ce, “Tashin hankali da ta’addancin da masu zanga-zanga da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai suka aikata a baya-bayan nan a fadin kasar, wanda ya haifar da shahadar daruruwan mutane da masu kare tsaron kasarmu kaunatacciyar Iran, a zahiri tsawaita yakin kwanaki 12 da Amurka da gwamnatin Sahayoniya suka shirya ne sakamakon gazawarsu.”

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta soki tsoma bakin Trump a harkokin cikin gida na Iran da kuma cin zarafin da ya yi wa al’ummar Iran, tana mai jaddada cewa dole ne ya jira martani mai zafi daga al’ummar Iran.

IRGC ta yi kira ga dukkan ‘yan Iran da su shiga cikin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a duk fadin kasar a ranar Litinin din nan.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa an kashe jami’an tsaro 109 a cikin tarzomar da aka yi a fadin kasar.

A wata hira da aka yi da shi a talabijin, Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce gwamnati tana nan don sauraron koke-koken jama’a na gaskiya, amma ya lura cewa akwai bambanci tsakanin zanga-zanga da tashin hankali mai tsanani da ake gani yanzu.

Pezeshkian ya yi gargadin cewa Amurka da Isra’ila ne ke jagorantar tashin hankalin yayin da suke neman “shuka rikici a kasar.”

Ya yi kira ga ‘yan kasar da su nisanta kansu daga “masu tayar da zaune tsaye da ‘yan ta’adda,” masu kashe mutane da kuma kona kadarorin gwamnati da masu zaman kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted