Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin gano da kuma lalata wani jirgin leken asirin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa a bakin mashigar ruwa ta Hurmuz a jiya Alhamis da yamma.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar IRGC reshen ruwa wato Navy na fadar haka a bayaninta na 16.
Bayanin ya bayyana cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata sojojin Amurka sun kasa zuwa da sojojinsu a bakin tekun farisa saboda tsoro don haka ne suke amfani da jiragen ruwa wadanda ake sarrafasu daga nesa, don ayyukan leken Asiri.
Labarin ya ce wannan karon sun aiko sun aiko da wani jirgin ruwa kan doron ruwa, wanda ake sarrafashi daga nesa saboda ayyukan leken asiri. Mai lamba 5838, jirgin ya isa bakin mashigar ruwa ta Hurmuz a lokacinda sojojin ruwa na dakarun suka gano shi suka kuma lalata shi.
Bayan haka dakarun sun bada sanarwan cewa an rufe mashigar ruwa ta Hurmuz har zuwa abinda hali yayi.