Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kakkabu wasu karin jiragen yakin Amurka samfurin Drones a sararin yankin tekun farisa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto IRGC na fadar haka a jiya talata, ya kuma kara da cewa Drones din masu suna LUCAS an kakkabosu ne a bandar Khamir da ke kudancin kasar a kuma bakin tekun Farisa.
Wannan dai yana daga cikin jerin hare haren da jiragen yakin Amurka suke ta yi a cikin yan kwanakin da suka gabata a yankin. Musamman a mashigar ruwa ta Hurmus.
Kafin haka a ranar litinin ma IRGC ta bada labarin cewa, sun kakkabo US MQM- 170
A kudancin tsibirin Qeshm banda haka ma, sun sauke wasujiragen daga sama ba tare da kakkbosu. Ba tare da sun lalace ba. Banda haka sun sami nasarar kama wasu jiragen ruwa karkashin ruwa tekun. Wadanda gaba daya asara ce babban ga Amurka a yakin da take fafatwa da JMI tun farkon wannan shekarar.
Labarin ya kammala da cewa jiragen yaki da kuma leken asirin samfurin MQ-9 kadai sun kakkabo har guda 55 tun fara yakin a cikin watan Fabrayrun da ya gabat.