Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran (IRGC) reshen NAVY ko ruwa sun bada sanarwar kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa wato Drones samfurin MQ-1 kan tsibirin Sirik wanda ya kawo adadin irinsa wadanda dakarun suka kakkabo zuwa 19 tun fara yaki a ranar 28 ga watan Fabrayrun shekara ta 2026.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ta nakalto bayanin da dakarun suka fitar a yau Asabar tana cewa, an kakkabo jirgin ne da tsarin garkuwan sararin samaniya na bai daya wanda rundunar ta samar a baya bayan nan.
Kafin haka a yau din rundunar IRGC ta bada sanarwan kakkabi jirgin yakin Amurka shima marasa matuki samfurin MQ-9 na 58 tun bayan fara yakin a dai dai mashigar ruwa ta Hurmuz.
Har’ila yau a jiya jumma’a ma, majiyar IRGC ta bada labarin lalata jirgin yakin Amurka samfurin F-16 a kusa mashigar ruwa ta Hurmuz wanda ya tilasta masa dakatar da ikinsa da kuma yayi saukar gaggawa a tashar jiragen sama na Al-Dhafra dake kusa da Abudhabi na UAE.