Dakarun kare juyin juya halin musulunci rashen rundunar Qudus tare da hadin kai da hukumar leken asiri na JMI da kuma yansandan kasa FRAJA sun sami nasar aiki tare a garuruwan Iranshahr, Khash, da kuma Saravan na yankin sistan baluchestan, inda suka halaka yan ta’adda har 13 sannan suka kama wasu da ransu suna kuma gudanar da bincike a kansu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa daga wadannan garuruwa uku ne yankin Sistan Baluchestan ne mafi yawan yanta’adda wadanda suke samun tallafin kasashen waje suke amfani da su don kawo hare-hare cikin lardin wadanda suka kai ga shahadar Jami’an tsaro da dama da kuma wasu fararen hula.
Jami’an tsaron sun kai sumamayen ne a safiyar yau Laraba, kuma babu wani jami’in tsaro da ya ji rauni ko ya rasa ransa a sumamen.