IRGC: Sabbin Jinin Hizbullah Ba Zasu Barin HKI Ta Numfasa Ba

Babban kwamandan dakarun QUdus na IRGC ya bayyana cewa sabbin mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun fara bada gudumawarsu wajen yakar sojojin HKI duk

Babban kwamandan dakarun QUdus na IRGC ya bayyana cewa sabbin mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun fara bada gudumawarsu wajen yakar sojojin HKI duk tare da shahadar shuwagabanninsu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Esma’il Qaani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, sabbin mayakan kungiyar Hizbullah sun fara lallasa sojojin HKI a yake yake na baya bayannan.

Janar Qaani ya bayyana haka a jawabinda da ya gabatar a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa, duk tare da shahadar shuwagabannin kungiyar Hizbullah a yake yaken na baya bayan nan amma dakarun kungiyar sabbin dauka sun ci gaba da yakin da shuwagabannin su ka yi. Yace a cikin yan kwanakin da suka gabata mayakan kungiyar sun lalata tankunan yaki na yahudawa har guda 20 a wani kauye a kudancin kasar Lebanon.

Yace tun bayan shahadar Sayyid Hassan Nasarallah, kungiyar ta lalata tankunan yakin HKI har 373 a cikin wannan lokacin. Ya ce a cikin wannan lokacin kashi 1/3 ne suka lalata, sannan wasu da dama lalace ta yanda ba zasu yi aiki ba sai an yi masu gyrarraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted