Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran reshen Ruwa ko Navy ya bada sanarwan cewa wani katafaren tankar dakon mai wanda yake kokarin sace hanya ya kuma wuce ta hanyar da ta sabawa doka a mashigar ruwa ta Hurmuz ya gamu da nakiyan ruwa wanda ya fashe ya kuma kama da wuta.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto sanarwan da IRGV Navy ta fitar yana cewa wannan shi makomar duk wani jirgin da yake son sabawa dokokin da hukumar (PGAS). Ya kuma kara da cewa wutan da y6a tashi yana da girma hatta wadanda suke bakin ruwa suna iya ganinsa.
Labarin ya kara da cewa jitgin dauke da danyen man fetur mai yawa ya kashe na’urorin gane shi da kuma sanin inda yake sannan ya kama wata barauniyar hanaya saboda wucewa ta mashigar ruwa ta Hurmuz amma ya gamu da abinda ya gamu da shiya kuma kama da wuta.
Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya san sunan jirgin da kuma na wace kasashe sannan daga ina ya taso.