IRGC: Karya Trump Yake Yi Kan Batun Tattaunawa Da Ita

Kakakin Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Iƙirarin shugaban Amurka na tattaunawar bayan fage da Rundunar Tsaron Juyin Juya Hali ruɗani ne

Kakakin Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Iƙirarin shugaban Amurka na tattaunawar bayan fage da Rundunar Tsaron Juyin Juya Hali ruɗani ne da ya samo asali daga shan kashi

Kakakin rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta (IRGC) ya musanta ikirarin shugaban Amurka Donald Trump cewa: Amurka tana gudanar da tattaunawa ta bayan fage da jami’an Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC game da batutuwan da suka shafi yaki, yana mai tabbatar da cewa wannan ikirarin ba komai bane illa ruɗani da ya samo asali daga shan kashi.

Birgediya Janar Hossein Mohebi, kakakin Rundunar IRGC, yana tsokaci kan ikirarin Trump tun da farko cewa: Amurka tana gudanar da tattaunawa ta bayan fage da jami’an IRGC kan batutuwan da suka shafi yaki, ya jaddada cewa: “Babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin jami’an IRGC da Amurkawa. Wannan karya da Trump ya yada ba komai bane illa kirkirar tunaninsa, sakamakon ruɗani da mafarkai marasa tushe da suka samo asali daga shan kashi da halaka a yakin da ake yi tsakanin kasashen biyu.”

Ya ƙara da cewa, “IRGC ita ce hannun al’ummar Iran da Jamhuriyar Musulunci, kuma tana faɗin ra’ayinta a fagen daga. Duk da haka, tattaunawar diflomasiyya tana ƙarƙashin ikon wasu sassa a cikin Jamhuriyar Musulunci. Kuma bisa bayanai da suka samu sun tabbatar da cewa; Jami’ai masu daraja a Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, a halin yanzu babu wata tattaunawa da suke yi da Amurkawa saboda rashin cika alƙawarinsu da kuma abubuwan da suka faru masu zafi sakamakon keta alƙawarin da Amurka ke yi akai-akai da kuma ci gaba da yi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted