Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da kame jirgin ruwa mai suna ” EPAMINIDES” wanda yake aiki tare da sojojin Amurka ‘yan ta’adda.
Sanarwar da irgc ta fitar ta kunshi cewa, bayan sa ido da bin diddigi na tsawon watanni shida da su ka gabata, wannan jirgin ruwa ya rika zirga-zirga uwa tasoshin jiragen ruwan Amurka.”
Haka nan kuma sanarwa ta ce, tuni an tsare jirgin ruwa saboda ya ki jin gargadin da aka yi masa sanadiyyar taka dokar kai da komowar jirgen ruwa a yankin.