Search
Close this search box.

IRGC:  Isra’ila ce ta tsara kisan Haniyah tare da goyon bayan Amurka

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin kasar Iran, Isra’ila ce ta tsara kuma ta aiwatar da shi da goyon bayan gwamnatin Amurka.

A wata sanarwa da ta fitar a yau  Asabar, rundunar ta IRGC ta bayyana cewa, harin ya hada da amfani da wani makami da aka harba mai dauke da sanadarai masu tarwasewa day a kai nauyin kilogiram bakwai, wanda daga bisani ya haifar da wata babbar fashewa.

Sanarwar ta kara da cewa an harba makamin ne daga wani yanki da ke wajen masaukin marigayi Isma’ila Haniyyah.

IRGC ta kuma sha alwashin daukar fansar jinin Haniyeh, inda ta yi nuni da cewa gwamnatin Sahayoniya ta ‘yan ta’adda za ta fuskanci hukunci mai tsanani a “lokaci, wuri da kuma yadda ya dace.”

Haniyeh wanda ya je Tehran domin halartar bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, tare da wasu shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya, ya yi shahada tare da mai tsaron lafiyarsa, a harin da aka kai a safiyar ranar 31 ga watan Yuli.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan matakin mayar da martani mai tsauri kan kisan gillar da aka yi wa Haniyya, yana mai cewa wajibi ne a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki fansa kan jinin jagoran gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas.

Jagoran ya ce “Masu aikata laifuka ‘yan ta’addar yahudawan sahyoniya sun yi sanadin shahadar babban bakonmu a kasarmu ta haihuwa kuma suka bar mu da bakin ciki, amma kuma Isra’ila  ta bude ma kanta kofar azabtar da kanta,” in ji Jagoran.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments