Wani babban Jami’in dakarun kare Juyin juya halin musulunci a nan Iran ya ce, sojojin sa a shirye suke su fuskanci duk wani harin ba zata daga makiya don kasar kasar, amma batun wai su kauda samuwar JMI, an kuma wuce wannan. Makiyamma sun yi kadan da yardarm All..su ga bayana JMI.
Burgedia Janar Yadollah Javani mataimakin babban kwamandan IRGC a bangaren harkokin siyasa ya bayyana haka a jiya Laraba a lardin Golistan na arewa maso yammacin kasar.
Ya kuma kara da cewa, akwai yiyuwar Amurka da HKI su sake farwa kasar da yaki, wanda ya fi na baya, tsanani, sai dai sojojin Iran da sauran Jami’an tsaro sun shiryawa masu, shiri mai kyau. Da yardarm All..abinda basu samu a cikin watanni kimani 8 da suka gabata ba zasu samu ba a cikin duk wani hare da zasu kawo nan gaba ba.
Yace idan sun sake wani kuskure to kuwa zasu sanya kansu cikin wasu matsalolin da ba zasu sake fita ba har’abada.
Javani ya kammala da cewa samuwar mutanen a kan titunan birnin kasar ya dagulawa makiya lissafi, saboda suna nan a madakata dare da ra, sannan sune suka zama garkuwa da gwamnati da kuma sojojin kasar wajen hana makiya samun abinda suke so.