Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na iran sun bayyana cewa tilas ne kasashen amurka da isra’ila su amince da yankin da ya kubuta daga shedana da muggan laifukansu ko ba dade ko ba jima
Dakarun sun fitar da wannan jawabin ne a wajen taron tunawa da cika shekaru 46 na kariya mai tsarki na yakin iraki da aka kakabawa kasar iran, kuma ta bayyana tsaro mai tsarki a matsayin wani shafi mai haske da daraja wajen samar da kudurin hadin kai tsakanin alumma, kuma makaranta ce ta dabarun samar da karfin tsaro da hana makiya ikon kai mata hari
Haka zalika sun kara da cewa dakarun sojin kasar suna cikin shirin ko ta kwana na mayar da martani kan duk wani wuce gona da iri da makiya za su yi, yace batun tsarkakkiyar kariya ta wuce batun ayyukan soji kawai ta kasance wani dandamali ne na samar da karfin alumma, hadin kan kasa da kuma dogaro da kai bisa tsari.
Daga karshe dakarun na IRGC sun yi gargadi cewa bayan shan kaye da makiysa suka yi a filin daga, yanzu sun koma yakin tattalin arziki da na farfaganda wanda a nan ma dakarunsu za su murkushe duk wani makirci da suke kullawa