Major General Mostafa Izadi ya ce idan makiya sun sake farwa kasar Iran da yaki, sojojin kasar zasu tsaya kan kare kasar nan, kuma zasu kori makiya ba zasu basu ko da inci guda na kasarsu ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin babban kwamandan IRGC ya kara da cewa sojojin Iran a shirye suke su fuskanci makiya ta sama da kasa da ruwa. Ya kuma kara da cewa wannan Amurka fa ta sha kaye a kasashen Afganistan da Iran.
Janar Izadi y ace, a yakin Iran da Iraki a farkon nasarar juyin juya halin musulunci Iran ta yake makiya na tsawon shekaru 8, daga shekara 1980-88, basu jada bayana ba. Duka da cewa makiya suna samun taimakon manya manyan kasashen duniya a lokacin. Sojojin Iran basu basu damar mallakar ko inci guda na kasar Iran ba har aka kawo karshen yakin.
Don haka a yau ma, zamu tsaya a gaban AMurka da HKI zamu saida rayukammu kamar yadda wadanda suka gabace mu suka saida rayukansu don kare musulunci don kare kasarmu. Sai mun samun nasara a kansu.
Daga karshe yace Amurka ta mamaye kasashen Afganistan da Iraki, na shekaru kimani 20 ko fiye da haka, amma sun kafa tabbata a kasar sun fice ba tare da sun cimma manufofinsu a wadannan kasashe ba. Me ya sa mu ba zamu tsaya ba mu kori makiya daga kasarmu.