Kakakin dakarun kare juyin musulunci na iran Brigadier Janar Hussain Mohebbi yayi wannan bayani ne a yau alhamis lokacin da yake bayyana irin karfin sojin da iran take da shi da kuma irin ci gaba da aka samu na makami mai linzami da ta sake kerawa bayan yakin kwanaki 12 da kwanaki 40 da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar iran a ranar 25 ga watan yuni da kuma na watan fabareru da ya gabata.
Muhebbi yace karfin ikon lalata makamai da aka yi amfani da su na dakarun kare juyin musulunci a yakin, yafi na wadanda aka ayi amfani da su a yake -yaken da suka gabata, ya kara da cewa Iran tana ci gaba da samun ci gaba a dukkan fannoni na makaman soji. kuma tana samar da makamai masu inganci da kuma ci gaba a fannin fasaha.
kakakin ya kara da cewa isra’ila tana yaki a gaza fiye da shekaru 2 amma har yanzu ta kasa yin wani tasiri a kokarin da take yi na rusa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas, don haka ba zai yi yu kasar saudiya wadda karfin sojanta bai kai na isra’ila ba ta iya yin nasara kan kungiyar gwagwarmaya ta Ansaralluh na kasar yamen.
Muhebbi ya jaddada cewa kungiyar Ansarullah a kullum tana kara karfafa karfinta na soja kuma dakarun yan gwagwarmayar sun ci gaba da samun ci gaba kuma suna kara yin karfi sosai.