Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Iran na nazarin wasu dabaru da za su tabbatar da aiwatar da shirin ta na kwanaki bakwai na sake bude mashigar ruwa ta Hormuz cikin lokaci mafi kankata, tare da kawo karshen takun-saka da Amurka.
A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta “ba wa diflomasiyya damar yin nasara,” duk da cewa tana “cikakken shirin kare kanta” daga duk wani sabon matakin cin zarafi ko hari.
Ya ce Iran na ci gaba da tattaunawa ta kut-da-kut da kasashen da ke shiga tsakanin Tehran da Washington, domin kawo karshen rikicin da ya shafi tsaron yankin da kuma samar da makamashi a duniya sosai.
A cikin sakon nasa, ministan ya nuna cewa Iran za ta iya hanzarta sake bude mashigar Hormuz, muhimmiyar hanyar wucewar makamashi da Iran ta sanya wa takunkumi tun farkon wannan shekarar, bayan da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka kai hari kan kasar.
Ya ce za a iya sake bude mashigar da wuri fiye da yadda aka tsara a cikin shirin kwanaki bakwai da Iran ta gabatar a watan Satumba.
A karkashin wannan shiri, wanda aka mika wa Amurka ta hannun kasar Qatar, Tehran za ta sake bude mashigar Hormuz tare da ci gaba da tattaunawa da Washington cikin mako guda, idan har aka amince da sharuddanta.
A cewar shirin, Amurka za ta kawo karshen hare-haren da take kai wa Iran, ta kawo karshen killace tashoshin ruwan kasar, ta sassauta takunkuman da aka sanya kan fitar da man fetur na Iran, sannan ta sako kadarorin kasar da aka daskarar—duk wadannan a cikin kwanaki biyar.
Bayan haka, a rana ta shida, Iran za ta sake bude mashigar Hormuz domin zirga-zirgar jiragen ruwan kasuwanci, sannan a rana ta bakwai ta ci gaba da tattaunawa da Amurka domin cimma yarjejeniya ta karshe.
Wadannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun tsaka tsakanin Tehran da Washington.
Iran ta yi gargadin cewa duk wani hari da Amurka da Isra’ila za su sake kai mata zai fuskanci martani mai zafi.
Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soja bayan zaben tsakiyar wa’adi na Amurka da za’a gudanar a ranar 3 ga waan Nuwamba mai shirin kamawa.