Iran Za Ta Rika Samar Da Megawatti 5000 Daga Tashar Nukiliya Ta Bushehr

Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Muhamamd Islami ya bayyana cewa nan gaba kadan Iran za ta rika samar da megawatti 5000 na wutar

Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Muhamamd Islami ya bayyana cewa nan gaba kadan Iran za ta rika samar da megawatti 5000 na wutar lantarki daga tashar Nukiliya dake Bushehr.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ ya ambato shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran yana cewa; Ba da jimawa ba, tashar ta Nukilkiya dake Bushehr za ta zama cikin Shirin da za ta iya bayar da wutar lantarki mai karfin megawatti 5000, tare da cewa, yin hakan yana a karkashin tsarin da ake da shi akan Shirin Nukiliya a Iran.

Har ila yau ya kara da cewa; A lokacin ziyarar da mu ka kai zuwa kasar Rasha, mun yi tattaunawa akan aiki tare a fagen fasahar Nukiliya.

Bugu da kari ya ce, alakarmu da kasar Rasha tana da kyau da akan haka ne mu ka gina tattaunawar da mu ka yi.

Kasashen Iran da Rasha sun kulla yarjejeniyar aiki ta tsawon shekaru 20 masu zuwa a cikin fagage da dama masu muhimmanci.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments