Search
Close this search box.

Iran: Za A Je Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa Tsakanin Jalili Da Pezeshkian

A kasar Iran za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu bayan da dukkanin ‘yan takarar suka kasa samun cikakkiyar nasara ta lashe

A kasar Iran za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu bayan da dukkanin ‘yan takarar suka kasa samun cikakkiyar nasara ta lashe zaben a zagayen farko, in ji kakakin hedkwatar zaben.

Mohsen Eslami ne ya sanar da sakamakon a ranar yau Asabar a wani taron manema labarai wanda gidan talabijin na kasar Iran  ya watsa bayan kirga kuri’u kusan miliyan 25 da aka kada.

Ya ce daga cikin kuri’u miliyan 24.5 da aka kammala kirgawa, tsohon ministan lafiya kuma babban dan majalisa Masoud Pezeshkian ya samu miliyan 10.4 yayin da tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kuma babban jami’in tsaro Saeed Jalili ya samu miliyan 9.4.

Sauran kuma wato kakakin majalisa Mohammad Baqer Qalibaf, da tsohon ministan cikin gida Mostafa Pourmohammadi, sun ci gaba da kasancewa a baya a kan mutane miliyan 3.3 da sama da 206,000 bi da bi.

Pezeshkian da Jalili za su fafata a zagaye na biyu na zaben da za a yi ranar 5 ga watan Yuli. Bisa ga dokar zabe ta kasa, ana zuwa zagaye na biyu ne idan babu dan takara da ya samu kashi 50 cikin 100 na dukkanin kuri’un da aka kada.

Ya zuwa yanzu Eslami ya fitar da bayanai  guda tara kan sakamakon zaben.

Sabbin bayanai na baya-bayan nan da misalin karfe 11:37 na ranar yau agogon kasar Iaran ya nuna cewa Pezeshkian na kan gaba da kuri’u 10,415,191 daga cikin kuri’u 24,735,185 da aka kirga ya zuwa yanzu. Jalili ya zo kusa da 9,473,298.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments