Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar ta bunkasa amfani da karfe ko a cikin gida sannan da wasu dabarbarun don saida su ga kasashen duniya.
Labarin ya kara da cewa yawan karshen da ake samarwa a cikin gida ya karo da kasha 34% a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara ta 2025, sannan yawan karfen da iran take satarwa zuwa kasashen wajen ya karu da kasha 45% a cikin wannan lokacin. Sannan tama ko danyen karfen da take sayarwa yin ninka idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
Banda haka karafunan (sheet) da ake mikesu sun kawowa kasar dalar Amurka miliyon $320. Kamfanin karafa ta Mobarakeh Steel da rassansa a kasar sun taka rawar a zo a gani wajen tabbatar da wannan ci gaban.