Iran: ‘Yan Wasan Taekwondo Mata Sun Sami Lambobin Yabo 7 A UAE

Kungiyar wasan motsa jiki ta matan Iran ta ” Taekwondo” dake halartar gasar da ake yi a UAE, ta sami kyautukan yabo 7 da su

Kungiyar wasan motsa jiki ta matan Iran ta ” Taekwondo” dake halartar gasar da ake yi a UAE, ta sami kyautukan yabo 7 da su ka hada zinariya da azurfa.

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; an bude wasannin ne na ” Taekwondo” ne a babban dakin taro na “Sheikh Zayid” dake birnin “Fujairah” da ya sami halartar masu gasa da juna 206 daga ciki har da ‘yan wasan Iran.

“Yan wasan na Iran sun sami lambar yabo ta zinariya 1, sai azurfa 3 da kuma tagullah 4.

Wadanda su ka wakilci Iran din sun hada; Mubinah Ni’imat Zadeh, a ajin nauyi na kilo 53, da ita ce ta sami zinariya.  Wadanda su ka sami kyautar Azurfa kuwa su ne Kausar Asase, a ajin nauyin kilo 62, da Saina Kirimi a ajin nuayi 46, da Fatima Ahmadi a ajin nauyi 73.

Wadanda su ka sami kyautar tagulla kuwa su ne Saina Alipur a ajin nauyi 46, sai Maryam Malakuti Khah a ajin nauyi 49, sai kuma Mulkiya Mir Husaini a ajin nauyi 73.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted