Wani mai ba da shawara kan soji na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) ya yi shahada a wani harin ‘yan ta’adda a kasar Siriya.
“Birgediya Janar Kioumars Pour Hashemi, wanda aka fi sani da Haj Hashem, daya daga cikin masu kare Haramin [Sayyada Zaynab] kuma babban mai ba da shawara kan soji a Syria, ya yi a wajen birnin Aleppo cikin dare,” in ji IRGC a wata sanarwa data fitar yau Alhamis.
Masu ba da shawara kan harkokin soji na kasar Iran da suke kasar Siriya bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi musu, sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Siriya wajen yakar ta’addanci da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dauwamammen tsaro a kasar ta Larabawa.
Tun a watan Maris din shekara ta 2011 ne dai kasar ta Siriya ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda daga kasashen ketare, inda Damascus ta ce kasashen yammacin turai da kawayen su na yankin suna taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda su yi barna a kasar Larabawa.
Isra’ila ta kasance babbar mai goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya tun bayan barkewar ‘yan ta’addar da ke samun goyon bayan kasashen waje a Siriya.