Iran: Trump Zai Iya Yin Nasara Ne Kwai A Cikin Tunaninsa

babban jami'in sojin kasar iran ya ce trump zai yi nasara ne kawai a cikin tunaninsa idan ya sake kaddamar da yaki kan kasar iran

Babban jami’in tsaro na kasar iran ya bayyana cewa  ikirarin da shugaban kasar Amurka Donald trump yayi na cewa ya samu nasara akan kasar iran ya zarta batun zato , yana nuna cewa alummar iran sojojinta da kuma makamai masu linzami ne ke iya tantance hakikanin yanayi da ake ciki a kasa

Mojor ganar Muhsen rezai babban sakatare majalisar kolin tsaro ta kasar iran yayi wannan bayanin ne a wani bayanin da ya wallafa a shafinsa na X yace bayan shan kashi daya bayan daya, mafi muni shugaban kasa da aka taba samu a tarihin Amurka ba shi da aiki sai dai surutai yanzu kalamansa sun wuce kalamai na kirkira

Wannan mayar da martani ya zo ne bayan da trump yayi ikirarin cewa amurka ta riga ta yi nasara ko kuma tana kan gargaran  yin nasara kan yakin da ta kaddamar kan kasar iran , kidaddigar baya bayan na da aka fitar ya nuna cewa ya maimaita cewa su ne suka yi nasara har sau 100,

Duk da ikirarin da Washington ta yi na cewa sun raunata sojojin kasar iran amma dakarunta sun ci gaba da kai hare hare da jiragen sama marasa matuki, da makamai masu linzami  kan sansanoni makiya tun daga wata juli, adai dai lokacin da amurka take ci gaba da kai hare hare kan kasar iran

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted