Iran Ta Yi Tir Da ‘Hannun Diblomasiyya’ Na Trump Bayan Farmata Da Yaki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaie yayi tir da shugaban kasar Amurka Donal Trump bayan ya bayyana cewa Amurka tana son ta sake

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaie yayi tir da shugaban kasar Amurka Donal Trump bayan ya bayyana cewa Amurka tana son ta sake shiga tattaunawa da Iran kan shirinta na makamashin nukliya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaie yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa shugaban ya yi wannan tayin a farkon shigabarsa fadar white house kuma munga matijar wanda itace yakin kwanaki 12 a cikin watan yunin da yagabata.

A jawabinsa a babban zauren MDD shugaba Trump ya bayyana  yadda jiragen yakin kasar samfurin B2 suka sauke boma-bomai har paund 30,000 a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar a Natanz da fordo da kuma Esfahan da nufin wargaza su. Amma masana sun tabbatar da cewa cibiyoyin basu lalace ba.

A lokacinda Trump yayi haka cibiyoyin uku suna karkkashin kulanahukumar IAEA masu kula da cibiyoyin Nukliya a duniya.

Trump ya zargi Iran da goyon bayan yan ta’adda a yankin , wanda kuma yake nufin Hamas da hIzbullah dakuma kasar Yemen da sauransu.

Baghaei ya bayyana cewa idan ka yi ishara ga wani to yatsu uku suna nun aka. Trump yana zargin Iran da goyon bayan yan ta’adda a yankin amma ya rufe idansa a kan abinda HKI take yi a gaza wannan dukkan duniya ta amince kissan kiyashi ne kuma ba don Amurka ba da hakan bai faruba.

Mutane a duniya suna da hankali sun kuma san waye dan ta’adda ko mai goyon bayan ta’addanci a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted