Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yayi allawadai da hare-haren da HKI ta kai a kan wurare daban daban a kasar Siriya wanda ya hada har da birnin Damascus babban kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Esma’ila Baqae yana fadar haka a safiyar yau Alhamis
. Ya kuma kara da cewa kasar Iran ta damu da rikicin da ke faruwa a yankin Suwaida na kudancin kasar ta Siriya wanda ya kai ga mutuwar mutane da dama a yankin.
Tasnom ta nakalto Baqae yana cewa abinda yah au kan kwamitin tsaro da kuma kasashen musulmi shi ne su tabbatar da cewa an sami tsayayyen gwamnati a kasar ta siriya wacce takem iko a kan kasar.
Amma a cikin wannan halin na rashin doka da oda, makiya musamman HKI ba zata taba barin mutanen kasar su zauna lafiya ba. Tun wannan ita ce ajendar kafata a kasar Falasdinu da ta ke mamaye da shi.
Kafin hare-haren yahudawan dai Hikmat al-Hajri
Shugaban daya daga cikin kungiyoyiun durus a yankinsuwaida ya bukaci mabiyansa su kaiwa sojojin HTS hare-hare wanda ya bar mukate da dama matattu ko sun ji rauni.