Iran, ta bayyana cewa tattaunawar da zatayi nan gaba da kasashen nan turai uku da aka fi sani da E3 zata kasance ne bisa hikima da kuma mutunci.
Da take sanar da hakan kakakin gwamnatin Iran din Fatemeh Mohadjerani, ta ce ganawar da mataimakin ministan harkokin wajen kasar zai yi da takwarorinsa na kasashen Turai, a ranar Juma’a za a yi ta a birnin Geneva, tare da la’akari da ka’idoji guda uku na mutunci da hikima da fahimtar kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya shata.
Madame Mohadjerani ta ce taron da zai hada mataimakan ministocin harkokin wajen zai gudana ne da kasashen Faransa, Jamus da Ingila.”
“Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi bangarorin biyu, shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma halin da ake ciki a Gaza da Lebanon, a cewar kakakin gwamnatin Pezeshkian.
A ranar Lahadi data gabata ce kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa kasar za ta tattaunawa da kasashen turan kan shirinta na nukiliya da ake ta takaddama a kai.
Ganawra na kuam zuwa ne ‘yan kwanaki kad abayan da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya fitar da sanarwar nuna damuwa kan abinda ya danganta da kumbiya kumbiya data dabaibaiye shirin nukiliyar Iran.