Iran: Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Hurmuz

Majiyar sojojin ruwa na JMI, ta bayyana cewa a jiya talata wani tankin dakon mai ya kama da wuta ya kuma lalace ya tsaya cik

Majiyar sojojin ruwa na JMI, ta bayyana cewa a jiya talata wani tankin dakon mai ya kama da wuta ya kuma lalace ya tsaya cik a lokacinda yake kokarin sace hanyar wucewa da mashigar ruwa ta hurmuz a jiya Talata.

Tashar talabijan ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto sojojin Ruwa na JMI na cewa jirgin ya kashe Na’urar gane shi sanan ya kama hanyar wucewa ta kudancin mashigar Hurmuz amma sai ya kama da wuta mai yuwa saboda nakiya, ya kuma lalace ya tsaya cik ya kasa. Tafiya.

Sanarwan da sojojin suka kara yana cewa duk wani jirnin da yake son wacewa ta Hurmuz dole ne ya bi ta hanyar da gwamnatin JMI ta ware don yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted