Iran Ta Raya Ranar Fada Da Kasashe Masu Girman Kai

A yau ne ake juyayi da kuma tunawa da wasu abubuwa har guda 3 a nan Iran daga ciki shi ne ranar fada da kasashe

A yau ne ake juyayi da kuma tunawa da wasu abubuwa har guda 3 a nan Iran daga ciki shi ne ranar fada da kasashe masu girman kai a duniya ta kasa. Tare da gudanar da jerin gwano zuwa tsohon ofishin jakadancin Amurka a nan Tehran.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Laraba 4 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2026, tubban mutanen kasar Iran wadanda suka hada da daliban makarantu firaimari da kuma na jami’o’ii suka fito kan tituna daban daban a nan birnin Tehran. Suke daga murya da ‘All..Ta ya kashe Amurk All…T ya kashe HKI Da Ingila. Duk sun hadu a tsohon ofishin jakadancin Amurka a nan Tehran.

Labarin ya kara da cewa a ranar 4 ga watan Nuwamban shekara 1979 daliban Jami’o’ii, masu bin tafarkin Imam Khumaini (q) suka kwace ofishin jakadancin Amurka da ke nan birnin Tehran, kasa da shekara guda da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.

Imam Khomaini (q) ya goyi bayan daliban jami;oin ya kuma bayyana abinda suka yi a matsayin juyin juya hali na biyu. Wanda ya fi na farkon. A lokacinda dai daliban sun kama jami’an diblomasiyyar Amurka har 52 suka tsaresu musamman bayan sun ganoi cewa Ofishin jqakadancin Amurka a Tehran cibiyar leken asiri na Amurka a yankin.

Har’ila yau a irin wannan rana ce, gwamnatin sarki sha ta tilastawa Imam Khomaini (q) gudun hijira daga kasar a shekara 1964 bayan ya zargeta da mika kai ga bukatun Amurka da kuma bautar da mutanen kasar Iran amma bayan shekaru 15 ya dawo ya kifar da gwamnatinsa sarkin.

Sai kuma Abu na 3 wanda shi ne kashe Taliban makarantu wanda gwamnatin sarki sha tari a lokacinda yake mulkin. A 4 ga watan Nuwamban shekara 1978.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted