A wani taron manema labaru da Muhammad Husaini Imani Khushkuh ya yi a birnin Tehran a jiya Asabar, ya bayyana cewa; Bangaren ayyukan al’adu na fasahohi masu alaka da ita, yana daga cikin fagagen da ba a bai wa muhimmanci sosai ba, a dalilin haka ne Iran din take shirin shiga da karfi cikin wannan fage a karkashin kungiyar kasashe masu tasowa ta “Bircks”.
Shugaban cibiyar kasar Iran mai kula da ilimi da kuma tsare-tsaren ayyukan al’adu da fasahohi masu alaka da su, ya kuma kara da cewa: Iran tana da abinda za ta fadawa duniya a fagen al’adu da fasahohi masu alaka da su, da hakan zai ba ta damar shiga cikin wannan bangare a karkashin kungiyar “Bricks”
Haka nan kuma ya ce cibiyar tasu ta yi azamar shiga cikin wannan fagen a matakin duniya domin tallata nata al’adun ga kasashe. Bugu da kari ya kuma ce; A nan gaba kadan Iran din za ta shirya baje koli a tsibirin Kish dake kudancin kasar, domin nuna cigaban da ta samu a wannan fage da rawar da yake takawa a cikin tattalin arziki na hanyoyin sadarwa na zamani.