Shugaban hukumar sararin samaniya na kasar Iran yace, kasarsa tana daga cikin kasashe 12 aduniya wadanda suke da fasahar ginawa da cilla tauraron yan’adam sanan kuma ta karbi bayanan daga tauraron sannan ta sarrafa bayanin don amfanin kanta da duk kawayenta a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto Hassan Salariyaeh yana fadar haka a jiya lahadi a garin Nishabur inda yake halattar bikin raya makon sararin samaniya ta kasa.
Salriyeh ya ce a cikin shekaru 2 da suka gabata masana a ma’aiukatar sadarwa ta kasar Iran sun gudanar da ayyukan masu muhimmanci da ya shafi sanarin samaniya sannan a karshen wannan shekarar da muke ciki zasu aiwatar da wasu karin ayyukan cilla taurarin yan adam wadanada zasu daga matsayin kasar a wannan magaren zuwa sama so sai.