Iran Tana Ci Gaba Da Mayar Wa Da Donald Trump  Na Amurka Martani

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakchi ya bayyana cewa; dakarun kasar a shirye suke domin mayar da martani akan keta hurumin kasarmu

ministan harkokin wajen Iran

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakchi ya bayyana cewa; dakarun kasar a shirye suke domin mayar da martani akan keta hurumin kasarmu

Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci na Iran din ya wallafa a shafinsa na X cewa; Wadanda su ka cutu daga faduwar farashin kudi, suna da hakkin yin hakan, sai dai kuma da akwai wadanda su ka fito domin yin tarzoma da ya hada da kai wa ofisoshin ‘yan sanda hari.”

Ministan harkokin wajen na Iran yana mayar da martani akan furucin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa za su kawo hari akan Iran, idan aka harbi masu zanga-zanga.”

Abbas Arakchi ya ce, shugaban kasar Amurka ya fi kowa sanin  cewa barnata dukiyar al’umma da ta daidaikun mutane, ba abu ne da za a lamunta da shi ba don haka ne  shi kanshi ya aike da dakarun tsaron kasa a cikin garuruwan Amurka.”

Haka nan kuma Abbas Arakchi ya ce, kamar yadda a baya al’ummar Iran su ka ki amincewa da tsoma bakin ‘yan waje cikin harkokinsu, a wannan karon ma ba za su lamunta ba ,tare da jaddada cewa, dakarun kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana,kuma sun san inda za su kai wa hari, idan aka keta hurumin kasarsu.

Shi kuwa wakilin jagoran juyin musulunci a cikin majalisar tsaron kasa, Ali Shamkhani, ya bayyana cewa; Iran za ta datse duk wani hannu wanda ya yi kokarin taba huruminta.

Dr.Ali Shamkhani ya ce, hurumin kasar Iran jan layi ne, ba abin wasa ko ciniki ba ne.

Shi kuwa shugaban hukumar majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; shiga da tsoma baki a harkokin cikin gidan Iran yana nufin rushe dukkanin manufofin Amurka a cikin wannan yankin.

Dr.Larijani ya ce; Da akwai banbanci a tsakanin ‘yan kasuwa da suke nuna rashin yarda da halin tattalin arziki, da kuma na masu tarzoma da barna, don haka Trump ya kwana da sanin cewa, shigar Amurka a cikin wannan batun, yana nufin hargitsa zaman lafiya a cikin wannan yankin da rusa ilahirin manufofin Amurka.”

Haka nan kuma Dr. Larijani ya yi kira ga al’ummar Amurka da su kwana da sanin cewa Trump shi ne wanda y afara wannan shiga sharo ba shanun, don haka su gargadi sojojinsu.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted