Wani jami’an gwamnatin kasar UAE ne zai isar da sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa Tehran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghani ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara na kasar UAE Anwar Gargash yana kan hanyarsa ta zuwa Tehran dauke da wasikar, don isar da ita ga jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei.
Labarin ya kara da cewa Gargash zai hadu da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da farko bayan isarsa birnin Tehran.
Kafin haka dai Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran siyasa, wanda ya je kasar UEA don halattar taron kwamitin siyasa na kasashen biyu ya gana da Gargash inda suka tattauna batun wasikar.