Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da dadewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka.
Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen yaki na kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata.
Mataimakin ministan ya bayyana cewa, Iran zata ci gaba da kasancewa cikin yarjeniyar NPT mai hana yaduwar makaman nukliya a duniya. Amma dokar da Majalisar dokokin kasar Iran ta kafa ta jingine hulda da hukumar IAEA ya sa Iran za ta sanya hulda da hukumar takaitacce shi dimma tare da wasu sharudda guda biyu. Gharib abada ya fadawa yan jaridu a birnin NewYork a ranar Laraban da ta gabata kan cewa tawagar ba zata kai ziyara cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ba. Sannan ya kammala da cewa hukumar makamashin nukliya na kasar Iran na lissafin irin asarorin da hare-hare Amurka suka yiwa cibiyoyin Nuklkiyar nkasar A Esfahan, Natansa da kuma Fordo.