Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan yayi watsi da duk wata tattaunawa da kasar Amurka kuma ya bayyanata a matsayin mara ma’ana, domin Amurka ta rika kai wa kasar Iran hari aduk lokacin da ake tattaunawa
Yace babbar matsalarmu da Amurka ita ce duk lokacin da aka hau teburin tattaunawa na dadanan sai ta kadamamr da yaki a akan mu, sun yi mana haka har sau 3, da haka ke nuna cewa su ba sa son tattaunawa kuma ya fadi hakan ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Armeniya a jiya litinin
A bangare guda kuma pezeshiyan ya yi kira da akara kyautata dagantaka tsakanin su da Yerevan, yace dole ne mu fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a bangaren kasuwanci kimiyya aladu da kuma kimiya da kuma bangarorin da zasu taimakawa juna.
A nasa bangaren minitan harkokin wajen arminiya mirzoyan ya jaddada game da irin ci gaban da aka samu a alakar iran da armeniya duk da takunkumin da aka kakaba mata.