Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatarsa ce take kula da dukkan al-amuran da suka shafi shirin makamashin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatarsa ce take kula da dukkan al-amuran da suka shafi shirin makamashin Nukliya na kasar, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta bukaci a jingine aiki da hukumar makamashin Nuikliya ta Duniya IAEA bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka suka kaiwa kasar.

Aragchi ya bayyana cewa mai yuwa nan gaba, majalisar koli na tsaron kasar ta kula da lamarin shirin makamashin nukliya ta kasar. Amma a halin yanzu tana hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar ne.

A jiya talata ce mataimakin babban sakataren hukumar makamashin nukliya ta duniya ya ziyarci Tehran, ya kuma tattauna dangane da yadda mu’amalar kasar zata kasance da hukumar.

Labarin ya bayyana cewa Iran zata ci gaba da aiki da hukumar ne tare da wasu sharrudda nana gaba. Amma har yanzun ba’a sanya lokaci da maida hulda da hukumar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments