Iran: Taadin Da Amurka Ke yi Na Barazana Ga Tsaron Makamashi

shugaban kasar iran yace ayyukan taadi da amurka ke yi na barazana ga makamashi na duniya

Masud pezeshkiyan shugaban kasar iran ya gargadin cewa mataken soji da kasar Amurka ta dauka a yankin tekun fasha yana barazana ga tsaron makamashi da kuma ci gaba tattalin arziki a yankin baki daya,

Da yake bayani a babban taron koli na kasashe masu arzikin iskar gas da ake gudanarwa a birnin mosko a yau talata shugaban kasar iran ya ja hankalin mahalarta taron game da kalubale da dama da kasuwar makamashi take fuskanta, musamman ma yayi nuni ga mummunan tasirin da hare haren wuce gona da iri na soji da kasashen waje ke yi kan zaman lafiya da kwanciyar hankali

 Yace harin da Amurka da hKI suka kai kan kasar Iran da ya afku a mataki biyu kuma adaidai lokacin da ake gudanar da tattaunawar siyasa yana daya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali da kuma hadari ga tsaron duniya baki daya

Daga karshe shugaban kasar iran pezeshkiyan yayi tir da matakin da Washington ta dauka na yi amfani da takunkumin tattalin arziki na ta’adanci  da kuma killacewa ta ruwa kan kasar iran, da kuma matsin lambar da take yi wa wasu kasashe na su biye mata wajen ayyukan da suka saba ma doka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted