Iran Ta Zo Ta Biyar A Wasannin  Kasashen Nahiyar Asiya

Wasannin da aka kawo karshensu a jiya Alhamis a garin Nagoya,'yan wasannin na Iran sun sami lambobin yaro na zinariya, azurfa da kuma tagulla.

A wasannin kasashen nahiyar Asiya da aka yi a kasar Japan, Iran ta sami kyautuka da su ka mayar da ita zuwa ta biyar.

Wasannin da aka kawo karshensu a jiya Alhamis a garin Nagoya,’yan wasannin na Iran sun sami lambobin yaro na zinariya, azurfa da kuma tagulla.

Dan wasan kokawa na Iran Ali Ridha Abdul wali ya sami kyautar zinariya a ajin nauyi na kilo 77, sai kuma Mahdi bali wanda ya sami tagulla a ajin nauyi na 97.

Shi kuwa Ridha Ali Pur ya sami azurfa ne a fagen hawan tsauni cikin sauri.

Wadannan lambobin yabon guda uku da Iran din ta sami ya mayar da ita zama ta biyar bayan da a baya ta sami wasu kyautukan 42 da su ka hada da zinariya 12 da azurfa 17, sai kuma tagulla 13. Kasashen da suke gaban Iran guda hudu su ne China, Japan, Korea Ta Kudu da Kuma Uzbekistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted