Iran ta zo matsayi na 3 a gasar Olympiad ta duniya ta shekarar 2024

Parstoday – Jamhuriyar Musulunci ta Iran tazo a matsayi na uku a jerin lambobin yabo na gasar Olympiad ta daliban duniya na shekarar 2024. Bayan

Parstoday – Jamhuriyar Musulunci ta Iran tazo a matsayi na uku a jerin lambobin yabo na gasar Olympiad ta daliban duniya na shekarar 2024.

Bayan kammala gasar Olympiad ta kimiyya ta 2024, a wasanni  guda 5 da suka fi daukar hankula a gasar (daga kasashe 53 zuwa 110), Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu matsayi na uku a duniya da lambobin yabo kala-kala har guda 22.

A rahoton Parstoday, Iran ta samu lambobin zinari 10 da azurfa 10 da tagulla 2 a wasannin Olympiad guda 5 kuma ta zo na uku a duniya.

A shekarar 2024, ‘yan kasar Iran sun sami nasarar lashe matsayi na farko a gasar Olympiad ta duniya ta ilmin taurari, matsayi na hudu a gasar ilimin sanin halittu da Physics, matsayi na takwas a Chemistry, matsayi na tara a na’ura mai kwakwalwa,  matsayi na goma sha takwas a Lissafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments