Tawagar yan wasan tekwando na maza daga kasar Iran sun zama zakara a gasar tekwando ta kasa da kasa wanda ke gudana a halin yanzu a garin Chonchun na kasar Korea ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa tawagar yan wasa daga kasashen 5 ne suka halarci gasar tekeando ta wannan shekarar ta 2024, kuma tawagar kasar Iran ta kunshi Mahdi Aabidini, Muhammad Hussain Yazdani, Ali Khooshravesh da kum Ali Fadhli Zandi.
Tawagar Iran a zagaye na kusa da karshe, sun kara da tawagar Ivory Coast kuma sun sami nasara akan su.
A gasa na karshe tsakaninsu da tawagar mai masaukin baki wato korea ta Kudu, tawagar Iran ta sami nasara a kansu a dukkan zagaye zagayen.
Banda haka a bangaren mata kuma a gobe Talata ce ake saran tawagar iraniyawa mata zasu fara tasu gasar tare da yan wasan korea ta kudu.