Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghae ya ti watsi da zargin kasar Faransa kan cewa It ace take son wargaza tsarin zaman lafiya a yankin kudancin Asiya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei yana fadar haka a nan Tehran, ya kuma kara da cewa, HKI ce abin zargim don nata laifuffukan sun sa kotun kasa da kasa ta fidda sammacin kama shuwagabanninta.
Amma kasar Iran yakamata a yabeta ne saboda kokarin da take yi na ganin zaman lafiya ta tabbata a kasashen yankin Asiya ta kudu.
Amma abin mamaki, shugaban Emmanuel Maocron na kasar Faransa, yana zargin kasar Iran da haddasa rikici a gabas ta tsakiya.
A wani bangaren, Macron ya zargi kasar Iran, dangane da shirinta na makamashin nukliya, inda Baqaie ya bayyana cewa, shirin nukliyar kasar Iran tana kan doka. Ya ce a cikin wannan halin HKI tana kissan falasdiawa tana kuma, fadada kasarta a yankin gabasa ta tsakiya, amma Macron ya rufe idanunsa daga halin da ake ciki a Gaza a yayinda mafi yawan kasashen duniya suna allawadai.