Iran ta yi watsi da sanarwar taron G7 kan shirinta na nukiliyar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya jaddada cewa shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya ne gaba daya, yana mai yin watsi da bayanin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya jaddada cewa shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya ne gaba daya, yana mai yin watsi da bayanin bayan taron kungiyar G7 game da shirin.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar , ta yi watsi da zargin da kungiyar G7 ke yi game da shirin Iran na nukiliya, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanaan ya yi kakkausar suka dangane da ikirarin  kungiyar G7, wanda ke nuna shakku kan yanayin ayyukan nukiliyar Iran.

Kungiyar G7 ta yi gargadi ga Iran cewa, za ta dauki wasu sabbin matakai idan Tehran ta mikawa kasar Rasha makamai masu linzami.

Kanaani ya soki zantukan G7 game da kudurin baya-bayan nan na nuna adawa ga Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta IAEA ta yi, yana mai cewa wani yunkuri ne na siyasa. Ya kara da cewa, wasu gwamnatocin suna keta hurumin tsari da ka’idoji na kasa da kasa, domin cimma burinsu an siyasa na kashin kai a kan kasashe masu ‘yanci kamar Iran.

Kanaani ya kara da cewa, Iran za ta ci gaba da yin mu’amala mai ma’ana da fasaha tare da hukumar IAEA bisa tsarin ayyukanta da hakkokinta, yana mai jaddada cewa Tehran ta ci gaba da jajircewa kan ayyukanta na nukiliya na zaman lafiya bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) duk da matsin lamba na siyasa da ake yi mata.

Ya alakanta tashe-tashen hankulan da ake fama da su a halin yanzu da matakan da Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa akwai bukatar wadannan kasashe su nuna kyakykyawar aniya, da kuma kaucewa ayyukan da suka shafi siyasa domin magance matsalolin da ke damun dukkan bangarorin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments