Wata kafar yada labarai ta kasar Amurka ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Maco Rubio na cewa ya bukaci Abbas Aragchi ministan harkokin wajen Iran ya gaggauta barin NewYork shi ya sa ya fice daga kasar a ranar Litinin sabanin shirinsu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin Iran a MDD na karyata rahoton Fox News na cewa Rubio ya fada masa cewa Aragchi da tawagarsa sun dade a NewYork kuma su gaggauta ficewa daga kasar.
Labarin ya kara da cewa, wannan labarin ba gaskiya ne ba, saboda ofishin Iran da ke NewYork ya rika ya shaidawa ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun kafin su bada Visar shiga kasar a ranar 17 ga watan Satumba dangane da ranar da zasu bar birnin NewYork kuma basu saba ba. Babu kuma wanda a gaggauta ficewarsu.
Ofishin jakadancin, ya kara da cewa, a lokacinda Amurka ta kasa samun abinda take so daga kasar Iran, ta hanyar kasar Qatar mai shiga tsakani ne ta koma kan zancen korar tawagar Iran zuwa taron MDD ta 81.
Y ace shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya gabatar da jawabinsa a babban zauren MDD a ranar 23 ga watan Satumba kuma a goben ya bar NewYork.
Amma Aragchi da tawagarsa sun ci gaba da zama a NewYork suna ganawa da shuwagabnnin kasashe da wakilansu da wasu kungiyoyi da yan jaridu har zuwa wa’adin da ke kan Visarsu suke fice ba tare da wani gaggauta ficewarsu ba.