Iran Ta Yi Watsi Da Ikirarin Amurka Da Burtaniya Na Hannu A Tashin Hankalin Bahar Maliya

Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da zarge-zargen da ya danganta da “marasa tushe ” da Amurka da Birtaniyya

Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da zarge-zargen da ya danganta da “marasa tushe ” da Amurka da Birtaniyya suka yi kan hannun Tehran wajen tada zaune tsaye a yankin Bahar Rum.

A cikin wasikar da ya aike wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da shugaban Kwamitin Sulhu, Amir Saeid Iravani ya mayar da martani ga ikirari da wakilan Amurka da Birtaniya suka yi, da wakilin gwamnatin Isra’ila suka gabatar  yayin bude taron kwamitin sulhu na MDD a ranar 30 ga watan Disamba.

Wakilin na Iran ya ce zarge-zargen marasa tushe da wakilin Isra’ila Danny Danon ya kawo tare da goyon bayan babbar kawarta Amurka, wani yunkuri ne na toshe munanen ayyukansu a yankin.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, kasarsa a matsayinta na mamba a Majalisar Dinkin Duniya, a kodayaushe tana yin aiki da abin da ya rataya a wuyanta na dokokin kasa da kasa da kuma tsarin MDD, tare da nisanta kanta da duk wani aiki da ya saba wa kudurorin kwamitin sulhun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments