Iran ta yi Allah-wadai da takunkumin da Amurka ta kakaba mata kan bangaren mai tana mai danganta takunkuman da harmtattu wadanda aka kakaba mata “ba bisa ka’ida ba “.
Amurka ta ce ta lafta wa Iran takunkuman ne saboda hare-haren data kai wa Isra’ila a ranar 1 ga watan Oktoba.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaïl Baghaï ya fitar, ya kare harin da Iran din ta kai kan Isra’ila tare da yin Allah wadai da sabon takunkumin na Amurka.
A ranar Juma’ar data gabata, Ma’aikatar baitul malin Amurka ta ce an tsara takunkuman ne da nufin kara matsa lamba kan Iran, gami da kayyade karfinta na samun kudaden shiga na makamashin da take amfani da shi don taimakawa masu gwagwarmaya a gabas ta tsakiya.
Sakatariyar baitul malin Amurka Janet L. Yellen ta bayyana cewa, “A matsayin martani ga harin da Iran ta kai wa Isra’ila, Amurka tana daukar kwararan matakai don kara dakile damar da gwamnatin Iran ke da shi na samar da kudade da kuma aiwatar da ayyukanta na tada zaune tsaye.”
Takunkumin na yau ya shafi kokarin Iran na samar da kudaden shiga daga masana’antar makamashinta da suka hada da bunkasa shirinta na nukiliya, da yaduwar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka,” in ji ta.