Arakchi: Mun dakatar da musayar sakonni tsakaninmu da Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, ya tabbatar da cewa an dakatar da duk wata tuntubar juna tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, saboda yanayin da ake ciki a halin yanzu a gabas ta tsakiya. Araqchi ya bayyana hakan ne a wannan Litinin a babban birnin kasar Omani, Muscat, inda ya […]

Hezbollah ta kai hari kan sansanin sojin ruwan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Haifa

Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan sansanin sojojin ruwan Isra’ila da ke Haifa, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da kai hare-hare kan kasar ta Lebanon. A ranar litinin da ta gabata ne wasu rokokin Hizbullah suka kai wa sansanin Stella Maris na gwamnatin sahyoniyawan […]

Rasha: Shugabannin kasashe 24 ne za su halarci taron koli na BRICS

Mataimakin shugaban kasar Rasha ya sanar da cewa shugabannin kasashe 24 ne za su halarci taron koli na kasashen BRICS a Kazan. Yuri Ushakov, ya sanar a wani taron manema labarai cewa, shugabannin kasashe 24 sun tabbatar da halartar taron na BRICS. A bisa rahoton Pars Today da ya nakalto kafar yada labarai ta BRICS, […]

Spain ta yi kira ga EU da ta dakatar da yarjejeniyar kasuwanci ta ‘Isra’ila’

Firayi Ministan Spain Pedro Sanchez, ya yi kira ga sauran mambobin kungiyar Tarayyar Turai da su goyi bayan bukatar Madrid da Ireland na dakatar da yarjejeniyar ciniki bisa tsarin Free Trade da aka kulla tsakanin kungiyar EU da “Isra’ila” saboda ayyukanta na yaki a Gaza da Lebanon. Spain da Ireland sun shafe watanni suna tattaunawa […]

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Oman A Birnin Mascat

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Omman Sayyid Badar Al-busa’idi a birnin Mascat babban birnin Omman a safiyar yau Litinin. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na fadar cewa ministan ya tattauna da tokwaransa na kasar Omman kan al-amura […]

Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Kai Sabbin Hare Hare Kan Wasu Wurare A HKI

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun kai sabbin hare hare kan wasu wurare masu muhimmanci a kasar Falasdinu da aka mamaye. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mayakan Hashdushabi na fadar haka a shafinsu na Telegram. Sun kuma kara da cewa sun yi amfani da makaman ‘Drones’ ko […]

HKI Ta Kona Falasdinawa Yan Gudun Hijira Da Ransu A Sansaninsu Da Ke Deir-balah

Sojoji HKI sun kai hare hare kan sansanin yan gudun hijira na Falasdinawa dake kusa da Asbitin Deir Balah, wanda yayi sanadiyyar tashin gobara mai yawa wanda ya yi sanadiyyar kona falasdinawa da dama wasu har mutuwa. Tashar tlabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hare haren wadanda sojojin yahudawan suka kai a […]

An Fara Taron Masu Gwagwarya Daga Kasashen Musulmi Da Dama A Nan Tehran

An fara taron kasa da kasa na masu gwagwarmaya musulmi daga kasashen duniya da dama a nan birnin Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa manufar taron itace tattauna hanyoyin taimakawa masu gwagwarmayan a kasashen yakin Asiya ta kudu da kasashe masu girman  kai a duniya. Da kuma Magana a kan […]

Jihar Kogi da wasu 15 sun ƙalubalanci sahihancin hukumar EFCC a gaban kotun ƙoli

hausa.premiumtimesng.Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya 22 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraren ƙarar da gwamnoni 16 na ƙasar suka shigar gabanta suna ƙalubalantar dokar da ta kafa hukumar Yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙi zagon ƙasa ta EFCC da wasu hukumomi biyu. Alƙalai bakwai ne za su saurari shari’ar a ƙarƙashin jagorancin Uwani Abba-Aji, […]

Iran : Yaki Ko Zaman Lafiya, Duk A Shirye Muke Mu_Araghchi

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa bata son yaki amma kuma a shirye ta ke ta kare hurimin kasarta. ”Muna shirye idan yaki ne, haka ma a shirye mu ke idan zaman lafiya ake so” Inji Ministan harkokin wajen aksar ta Iran Seyyed Abass Araghchi. Ya bayyana hakan ne ga manema […]

Pezeshkian Da Macron, Sun Tattauna Kan Halin Ake Ciki A Yankin

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun tattauna ta wayar tarho kan hanyoyin kawo karshen rikici a yankin da kuma samar da tsagaita wuta a Lebanon. Shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin musamman yadda rikicin kudancin kasar Labanon ke kara ruruwa. A yayin […]

Harin Hizbullah Ya Kashe Sojojin Isra’ila 4 A Wani Sansanin Soji

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta dauki alhakin hari kan wani sansanonin sojin Isra’ila, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar soji hudu tare da jikkata wasu da dama. Hezbollah ta fada a ranar Lahadin cewa, ta harba wani rukunin jiragai marasa matuki a sansanin horas da sojoji na Isra’ila a yankunan arewacin da ta mamaye. Ma’aikatar […]

Guteress : Hari Kan Dakarun MDD, Zai Iya Zama Laifin Yaki

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, hare-haren kan dakarun wanzar da zaman lafiya na iya zama ‘laifi na yaki’. “Hare-hare” kan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kan iya zama “laifukan yaki”, kamar yadda kakakin babban sakataren MDD ya yi gargadi, bayan wani sabon taho mu gama da akayi tsakanin sojojin […]

Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata A Bangaren Man Fetur

Iran ta yi Allah-wadai da takunkumin da Amurka ta kakaba mata kan bangaren mai tana mai danganta takunkuman da harmtattu wadanda aka kakaba mata “ba bisa ka’ida ba “. Amurka ta ce ta lafta wa Iran takunkuman ne saboda hare-haren data kai wa Isra’ila a ranar 1 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da […]

Rikicin Sudan Ya Yi Ajalin Rayukan Mutum 30 A Cikin Kwanaki Biyu

Rahotanni daga Sudan an cewa mutane sama da talatin ne suka rasa rayukansu kana wasu da dama suka jikkata a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah Al Burhane da na Janar Mohamed Hamdane Daglo. Bayan harin bam da aka kai a wani masallaci a ranar Juma’a 11 ga watan […]