Iran ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri na kawancen Amurka da Birtaniya kan kasar Yemen.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Amurka da Birtaniya da Isra’ila suka kai kan lardunan Sanaa, Al-Hudaydah da Amran na kasar Yemen.
A cikin wata sanarwa, Baghaei ya yi tir da hare-haren kan kayayyakin more rayuwa da na fararen hula na Yemen, wanda ya zo daidai da gagarumar zanga-zangar da aka yi a kasar Yemen domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi a Gaza.
Ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin kololuwar keta doka da oda da kuma dokokin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma jaddada nauyin shari’a da ke wuyan dukkanin gwamnatoci da cibiyoyin kasa da kasa da na Musulunci don dakile ci gaba da kisan kiyashi da keta hakkin bil’adama na kasa da kasa a yankunan Palastinawa da aka mamaye.