Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar da wata sanarwa tana mai Allah Wadai da barazanar Amurka na sanya takunkumin hana safarar man fetur din Venezuela tana mai danganta matakin da marar ma’ana.
Iran ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta cin zarafi da amfani da karfi,” wadda ya zama keta dokokin kasa da kasa, da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, da kuma ka’idojin ‘yancin zirga-zirga da cinikayyar kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta bayyana cewa duk wani yunkuri na Amurka na kamewa, ko hana zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci shiga ko fita daga Venezuela wani “fashi da makami ne da gwamnati ke daukar nauyinsa a teku.”
Ta kara da cewa, “Babu wata kasa da ke da ikon tsoma baki a harkokin cikin gida na Venezuela.”
A cewar Iran idan Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya ba su mayar da martani ba, irin wadannan ayyuka za su kafa tarihi mai hadari kuma su hadassa rashin zaman lafiya a kasashen duniya.
A Ć™arshe, ma’aikatar ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Kasashen ‘yan ba ruwanmu (NAM) da duk gwamnatocin da ke da alhaki da su yi Allah wadai da haramtattun ayyukan Amurka na keta dokokin kasa da kasa.